Yadda majalisar dattawa ta amince Buhari ya bawa yahaya bello biliyan 10

A yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da zabe na da kwanaki 2 a  jahar Kogi,majalisar dattawan Najeriya ta amince da biyan gwamnatin jahar ta Kogi naira biliyan 10.

A watan Oktoba ne shugaba Buhari ya nemi izinin majalisar dattawa, a wata wasika da ya aika, na biyan gwamnatin jahar Kogi naira biliyan 10 na basussukan da suke bin gwamnatin tarayya na gudanar da ayyuka mallakan gwamnatin tarayya.

An yi cece-kuce a zauren majalisar yayinda Sanatocin jam’iyyar adawa ta PDP suka nuna rashin yardarsu da biyan kudin a wannan lokaci.

Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu wato  Enyinayya Abaribe, yayi magana a madadin dukkan sanatocin jam’iyyar, inda ya  bukaci majalisa ta dakatar da biyan kudin zuwa mako mai zuwa bayan an kammala zabe.

Sai dai  shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, bai amince da hakan ba, inda yace jahar Kogi ta nemi kudin tun zamanin Saraki amma aka ba’a basu ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More