Yadda majalisar ta rabu biyu kan kafa sabbin masarauta a Kano

Menene ra’ayin ku game da hakan?

Bukatar da gwamnan jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya mika gaban majalisar dokokin jahar Kano ta neman su tattauna tare da amincewa da kudurin dokar kafa sabbin masarautu guda 4 a jahar ta raba kawunan yan majalisar.

Ganduje ya sake aika wa majalisar kudurin dokar kafa sabbin masarautun ne bayan wata kotu a Kano ta rusa masarautun sakamakon kura-kurai da tace an tafka a yayin da ake samar da dokar kafa masarautun tun da farko, wanda haka yasa gwamnan ya sake sabon shiri.

Idan har majalisar ta amince da kudurin dokar har ta tabbatar da shi kamar yadda gwamnan yake muradi, dokar za ta bashi daman kafa masarautu guda 4 masu daraja ta daya wanda zasu yi gogayya da masarautar Kano ta Sarki Muhammadu Sunusi wajen matsayi.

Sai dai The Nation ta ruwaito cewa,an kasa samun daidaito tsakanin yan majalisun, inda suka kwashe tsawon sa’o’i uku suna tafka muhawara game da kudurin har ma ta kai ga an koma cacar baki, haka kuma aka tashi barambaram ba tare da an cimma wata matsaya ba.

Hakkan yasa shugaban majalisar ya dage cigaban tattauna al’amarin zuwa ranar Alhamis 5 ga watan Disamba 2019. Duk da cewa zaman sirri majalisar ta yi yayin tattauna kuduri, amma rahotanni sun tabbatar da cewa an hana yayan jam’iyyar PDP dake majalisar tofa albarkacin bakinsu game da dokar, sakamakon duk kokarin da suka yi na neman a basu izinin yin magana ya ci tura. Kuma da yake yan PDP 12 ne kacal majalisar, hakan na nufin basu da tasirin kawo ma dokar kancal saboda yawansu bai taka kara ya karya ba a idon doka, basu kai adadin biyu bisa uku da nema wajen samun rinjaye ba, don haka idan har kan yayan jam’iyyar APC ya hadu a kan wannan kuduri, magana ya kare.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More