Yadda masu garkuwa da mutane suka yi awun gaba da diyar dan majalisa a Kano

Wasu masu garkuwa da mutane sun sace ‘yar gidan dan Majalisar Dokoki ta Jahar Kano mai wakiltar Karamar Hukumar Dambatta, Alhaji Murtala Musa Kore da  tsakar daren ranar Asabar.

‘Yan bindigar sun dauki Juwairiyya ne da misalin karfe 3:00 na dare bayan sun yi yunkurin yin garkuwa da mahaifinta amma sai suka tarar ba ya nan.
Jamilu wanda dan uwa ne a wajen Juwairiyya ya shaida wa BBC cewa, mahaifinsu yana birnin Kano a lokacin da ‘yan bindigar suka shiga gidana nasu da ke kauyen Kore a Karamar Hukumar Dambatta.

Juwairiyya Murtala Musa mai shekara 17, daliba ce ‘yar aji biyar a makarantar sakandare ta Government Secondary School Jogana kuma ita ce ‘yar auta a wurin mahaifin nata.

“Mutum uku ne suka fara shigowa cikin gidan amma ba mu san yawan wadanda suka tsaya a waje ba,” in ji Jamilu.

“Sun ajiye motarsu nesa da gidan, saboda haka ba mu iya ganin inda suka yi ba.”

Ya kara da cewa da farko sun kama yayan mahaifin nasu kuma suka daure shi bisa zaton shi ne Honarabul Murtala.

Ana dai ci gaba da samun matsalar garkuwa da mutane a Najeriya musamman jahohin arewa maso yamma.

Duk da cewa ba a cika samun rahotannin garkuwa da mutane a jahar Kano ba kamar takwarorinta na sauran yankin, masana tsaro na ganin cewa idan ba a yi maganin abin ba bayan lokaci kadan wannan matsala kan iya mamaye ko ina.

Ko a kwanakin baya sai da ‘yan bindiga suka sace matar wani dan majalisa a jahar Jigawa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More