Yadda Najeriya Ta Lallasa Guinea A Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya wato “Super Eagles”, ta lallasa takwararta ta Guinea Conakry da ci 1-0 a wasan rukunin B na gasar cin kofin kasashen Afrika da ke gudana a kasar Masar.

Najeriya ta ci kwallon ne ta hannun Kenneth Omeruo a minti na 73.

Nasarar dai ita ce ta biyu da tawagar  yan Najeriya ta samu a gasar, wadda ke nufin ta samu damar tsallakawa mataki na gaba, duk da cewa akwai wasa daya na rukunin da ya rage mata dan cigaba da wasannin.

Da hakkan ne Najeriya ta hada maki shida a wasa biyu, bayan da ta ci Burundi 1-0 ranar Asabar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More