Yadda PDP ke tantance yan takarar su kan zaben Kogi da Bayelsa

Jam’iyyar PDP ta fara tantance ‘yan takarar da za ta basu tikitin tsayawa takarar gwamnan jahar Kogi da jahar Bayelsa a zaben gwamna da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamban 2019,a offishin yakin neman zabe na  PDP dake maitama dakuma shedikwarta PDP dake babban birnin tarayyar Abuja a ranar Litinin 19 ga watan Agusta.

Yan takarar daga jahar Bayelsa yanzu haka ana tantancesu ne a babban shedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, a yayin da kuma ‘yan takarar na jahar Kogi suke amsar tantancewar a Legacy House, ofishin yakin neman zaben shugaban kasa da ke Maitama, Abuja.

Gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku shine Shugaban kwamitin tantance ‘yan takarar na jihar Kogi,  a yayin da kuma gwamnan jahar Oyo, Misis Seyi Makinde ya kasance shugaban kwamitin tantance ‘yan takarar daga jahar Bayelsa.

Da yake ganawa da yan jarida kan tantancewar, gwamna Makinde ya tabbatar da cewar wannan tantance yan takarar za su gudanar da shi bisa gaskiya da adalci domin ciro wadanda za su tsaya wa jam’iyyar har su kai ga samu nasara, sannan  ya tabbatar da cewar za su yi kokarin hada kan ya’yan jam’iyyar ba tare da jawo baraka ba domin tabbatar da cewar sun lashe kujerun da zaben da ke gabatowa.

Ba mu fatan samar da yanayin da zai kai ga raba kan ya’yan jam’iyyarmu har zuwa lokacin zabe.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More