Yadda Rotimi Amaechi ya tsalake rijiya da baya a kasar Spain

Menene ra’ayin ku game da hakkan?

Ministan Sufuri na kasar Najeriya  Rotimi Amaechi, ya tsalleke rijiya da baya, yayin  da wasu yan Najeriya mazauna kasar Spain suka kai masa hari,a lokacin da ya je dan wakiltar Najeriya a taron sauyin yanayi a Madrid dake kasar Spain.

Sai dai bayyana  cewa, amma kafin a yi min illa, yan sandan Spain sun yi gaggawar shiga tsakani. Kuma babu abin da ya same ni, inda yayi godiya da gayon bayan da yasamu tare da addu’o’in magoya bayan nasa.

Amaechi ya fitar da sanarwar  hakan ne a shafinsa an Twitter a ranar yau Juma’a 6 ga watan Disamba 2019.

Hakkan  dai ba shi ne karon farko da yan Najeriya mazauna wasu kasashen waje ke kai hari kan manyan jami’an gwamnati ba.

Watannin baya da suka wuce, an zargin masu kokarin kafa kasar Biafra, sun far wa tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa wato  Ike Ekweremadu a kasar Jamus.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More