Yadda ta kaya a kotu sakamakon Maina ya kamu da  rashin lafiya

An samu cikas wajen gurfanar tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho AbdulRashid Maina, gaban alkalin babban kotun tarayya dake Abuja, Alkali Okon Abang, a yau Talata 5 ga watan Nuwamba,sakamakon rashin lafiya.

Hukumar EFCC ta kai karar Maina kotun ne bisa  zargin almundahana, babakere da yaudara na kudin fanshon jama’a kimanin kudade har naira Biliyan dari.

Jami’an hukumar gidajen yarin da sauya hali sun gabatar wa alkalin kotun, takardar likitan gidan yarin mai suna Idowu Ajayi, cewar wanda ake tuhuma da laifin wato, Maina ya kamu da rashin lafiya

Bayan karanta wasikar, Alkali Okon Abang ya tambaye lauyoyin EFCC da na Maina ko sun san da rashin lafiyar tasa, yayin da dukkansu suka ce basu da labara hakan.

Lauyan Maina ya bukaci kotun ta dage da zaman zuwa sati daya domin ya samu lafiya.

Sai dai  lauyan na EFCC Mohammed Abubakar, ya bukaci kotun ta umurci mataimakin kwantrolan hukumar gidan yarin ya je ya duba Maina domin tabbatar da gaskiyan lafiyarsa.

Inda alkalin ya yanke cewa takardar likitan ba zai hana cigaba da gurfanar da shi ba a gaban kotun, duba da cewa likitan bai sa lokacin da ake sa ran zai samu lafiya ba.

A karshe  dai an dage zaman kotun zuwa ranar Alhamis 7 ga Nuwamba 2019.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More