Yadda ta kaya tsakanin kungiyar kwadago da gwamnati

Shugabannin Kungiyar Kwadago ta Najeriya da wakilan gwamnatin kasar sun cimma matsaya kan mafi karancin albashi na naira 30,000 a safiyar Juma’a 18 ga watan Oktoba 2019, kamar yadda karamin ministan kwadago Festus Keyamo ya bayyana.
Bayan tattaunawar da aka kwashe kusan kwana uku ana yi, shugabannin kungiyar da wakilan gwamnati sun kin amincewa kan lamari guda da ya shafi tsare-tsaren albashi 12 na ma’aikatan gwamnati.
Yarjejeniyar ta amince cewa ma’aikata da ke mataki na 7 zuwa na 17 za su samu karin albashi tsakanin kashi 14 zuwa kashi 23 cikin 100, yayin da wadanda ake biya albashi na musamman da ake kira CONHESS za su samu karin albashi na kashi 23.3 zuwa kashi 10.5 cikin 100 a mataki guda.
Kafin a cimma matsayar, kungiyar kwadagon ta bukaci a yi wa ma’aikatan da ke karbar albashin da ya haura naira 30,000 karin kashi 29 cikin dari da wadanda suke mataki 11 ziwa 17.
Mafi karancin albashi na Naira 30,000 ya zama doka a Najeriya tun a watan Afrilun 2019 amma yadda manyan ma’aikatan gwamnati za su amfana da sabon tsarin ya sa gwamnati da kungiyar kwadagon tattaunawa tun ranar Talata don gujewa fadawa yajin aiki.
Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da Kungiyoyin Kwadagon na NLC da TUC ne bayan da suka yi barazanar fara yajin aiki ranar 16 ga Oktobar 2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More