Yadda wata mata yar Najeriya ta haihu a jirgin sama kuma jirgin ya juya bayan ya tahu kasa Najeriya

Jirgin da ya kwaso ‘ƴan Najeriya daga Dubai ya koma bayan wata mata ta haihu a cikinsa jim kaɗan da tashin jirgin dan isa birnin Legas.

Sanarwar da hukumar da ke kula da ‘ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta fitar, ta ce matar ta haifi namiji a cikin jirgin Emirates da ke ɗauke da ‘ƴan Najeriya, minti 30 bayan  barowar sa kasar ta Dubai.

Sanarwar ta bayyana cewar,
Dalilin hakan jirgin koma  Dubai.  Sannan kuma matar tana asibiti  ana kula da lafiyarta da ta jaririnta waɗanda ke cikin ƙoshin lafiya.  Inda kuma aka sauya jirgin, kuma ya taho hanya zuwa Legas ɗauke da ƴan’ Najeriya guda 265.  A ranar Talata ne ma’aikatar ƙasashen waje ta Najeriya ta ce za ta fara kwashe ƴan kasar da suka maƙale a wasu ƙasashe sakamakon hana tafiye-tafiye saboda annobar Coronavirus.

Ta ce za a kwaso tawagar farko ta ‘yan Najeriya 265 ne daga Dubai a ranar Laraba, sannan kuma a kwaso mutum 300 daga kasar ta Landan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More