Yadda yan bangar siyasa suka kona shugabar mata ta PDP kurmus a jahar Kogi

An zargin yan bangar siyasa ne suka kona wata mata a gidanta da ke Ochadamu, karamar hukumar Ofu da ke jahar Kogi kurmus.Abun ya faru ne bayan zaben gwamnan da aka gudanar na ranar Asabar din data gabata a jahar

Matar mai suna Acheju Abuh itace shugaban mata ta jam’iyyar PDP a gundumar Wada/Aro na yankin.

Iftila’in ya faru ne a ranar Litinin da rana bayan da yan dabar sun  zarge ta da yin biyayya ga jam’iyya mai mulki.

A gano cewa, ‘yan daban sun kutsa cikin gidan matar ne da wajen karfe 2 na rana inda suka rufe duk wata hanya da zata iya fita. Sun watsa fetur a gidan tare da kunna wuta.

‘Yan dabar da ake zargin sun hana mutanen yankin kaiwa matar taimako sakamakon harbin da suka dinga wanda ya tsorata mutane duk suka tsere. Hankulan ‘yan daban bai kwanta ba har sai da suka ga gidan ya kone kurmus.

Matar ta yi yunkurin gudu ta taga amma ta kasa saboda karafuna da ke tagar tare da harbin da suka dinga aunawa ta inda take. Gawarta na ma’adanar gawarwaki ta asibitin koyarwa na Anyigba don bincike.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan jahar Kogi William Aya, ya tabbatar faruwar  al’amarin.

Ya ce, sun samu rahoto ne daga wani mutum mai suna Musa Etu a karamar hukumar Ofu din da wajen karfe 4:30 na yamma a ranar 18 ga watan Nuwambar.

Tashin gobarar ta shafi wasu gidaje uku da ke da makwaftaka da gidan matar.

Jami’an yan sanda tare da jami’ai na musamman suna wajen da abun ya faru don hana cigaban tashin-tashinar hankulan al’ummar yanki, yayin da kuma ake cigaba da binciken wayanda suka aikata badakalar.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More