Yadda zaman Buhari da sabbin Ministoci ya kasance a wajen bitar sanin makamar aiki

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya shaida wa sababbin ministocinsa masu jiran gado cewa, gwamnatinsa za ta laru kuma ya dogara da su wajen aiwatar da manufofin da fadarsa ta tsara wa gwamnatinsa wajen cimma nasarorin da su ka saka a gaba na kafa harsashin cigaban Najeriya a cikin shekaru takwas da zai karasa yana mulkar kasar.
 
Buhari ya yi wannan tambihi ne a wajen biki bude bitar sanin makamar aiki wanda aka shirya yin sa a kwana biyu yayin da aka gudanar da bitar ga sabbin ministocin a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin 19 ga watan Agusta 2019.
 
 
Shugaba Buhari ya taya sababbi da tsofaffimn ministocin murna ya kuma kara da cewa, an shirya taron ne domin wayar mu su da kai da kuma dora su bisa tafarkin manufofin da gwamnati ta tsara zata aiwatar, a zangon mulkin na biyu, inda za su kafa harsashin fitar da ’yan Najeriya Miliyan 100 daga cikin fatara da kuncin talauci.
 
 
Ya kuma bayyana cewa, abubuwa uku gwamnatinsa ta sanya a gaba, wadanda su ne za ta fifita a gabadayan zamanin mulkin nasa.
 
Tun a zangon farko mun zayyana bangarori uku da mu ka fifita, wadanda su ka hada da tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa,” in ji shugaban.
 
 
Ya cigaba da ikirarin cewa, gwamnatinsa ta cimma gagarumar nasara a wadannan fannoni, inda su ka kora ’yan ta’adda maboyarsu, su ka tara ajiyar asusun waje tare da tsaida hauhawar farashi a kasar, baya ga kwato biliyoyin Naira da a ka sace daga baitulmalin Najeriya.
Sannan  ya hankaltar da ministocin da cewa, “duk da dai an zabo ku ne, don ku wakilici jahohinku kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, amma ku sani cewa, Najeriya za ku yiwa aiki gabadayanta.
 
Inda a karshe shugaba Buhari ya jaddada cewa, alhakin tafiyar da ma’aikatun da a ka ba su ya dogara ne kacokan a kansu.
 
 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More