Yahaya Bello na iya lashe zaben mai zuwa – Wasu yan PDP a Kogi Shin kuna ganin hakan take?

Alamu na nuna cewa jam’iyyar hamayya ta PDP ta samu kan ta a rikicin cikin gida bayan zaben da ta yi wajen tsaida dan takarar gwamna a jihar Kogi inda wasu ke neman sauya-sheka a yanzu. PDP ta samu kan ta cikin matsala ne a jahar Kogi tun bayan da Injiniya Musa Wada ya lashe tikitin takarar gwamna a zaben 2019.

Wannan na iya ba gwamnan APC dama ya ci gaba da mulki. Wasu Jiga-jigan PDP sun fara nuna shirin su na komawa APC ko kuma su tsaya a cikin gidan su yi wa jam’iyyar barna domin kowa ya rasa. ‘Yan takara da-dama sun fusata da zaben cikin gidan.

Wani babban Jigon PDP a yankin yammacin Jahar Kogi ya fadawa ‘yan jarida cewa jam’iyyar ta na cikin wani hali war haka, inda Jigon jam’iyyar ya kyankyasa cewar PDP ba za ta kai labari a babban zabe ba da yake gabatowa na watan Nuwanbar nan ma zuwa.

Yayin da jigon PDP ya koka da yadda aka wulakanta daya daga cikin masu neman kujerar gwamnan Kogi a PDP watau Abu Ibro wato dan tsohon gwamna kuma kusa a jahar ta Kogi.

Har ila yau daya daga cikin yan takarar ya koka da yadda aka yi watsi da irin su Abubakar Ibrahim Idris saboda wasu na jin haushin Mahaifinsa.

Hakan yasa wasu fara shirin sauya-sheka. Daga cikin wadanda su ka nemi mulki a jam’iyyar PDP su ka rasa, akwai wadanda yanzu sun fara yin kus-kus da gwamna Yahaya Bello. Hakan na nufin su na daf da shirin yi wa PDP zagon-kasa. Akwai dan takarar da yake kukan cewa an yi rashin adalci wajen hanasa tutar gwamna a 2015, sannan kuma aka dauki tikitin da ya dace a ba shi, aka mikawa Dino Melaye a zaben bana. Sanata Dino Melaye wanda ya bar APC a bara ya kuma samu takara a PDP ya na cikin wadanda su ka nemi tikitin gwamna a zaben da aka yi kuma ya na cikin fusatattun ‘ya ‘yan jamiyyar a yanzu. Injiniya Wada Musa wanda PDP ta tsaida shi ne zai kara da gwamna mai-ci Yahaya Bello a zaben da za ayi cikin tsakiyar Nuwamban 2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More