Yahaya Bello yayi murna da hukuncin kotu kan sake zaben na Dino

Gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello, ya bayyana farin cikinsa kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke game da zaben kujerar Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma,  wajen yin watsi da zaben Sanata Dino Melaye.

A cikin shari’ar da kotun tayi a safiyar yau Juma’a 11 ga watan Oktoba 2019,  ta sake tabbatar da hukuncin kotun zabe inda ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta sake gudanar da wani sabon zabe.

Yahaya Bello da Dino Melaye sun kasance abokan adawar juna a siyasance na tsawon shekaru uku kenan yanzu, wadanda a da kuwa suke karkashin inuwa daya a siyasar.

Mai magana da yawun bakin gwamnan wato Mohammed Onogwuya, ya fitar da cewar,   abinda kotun zaben ta fadi na cewa PDP ta tafka magudi a zaben ya tabbata yanzu.

Gwamnan jahar ta Kogin   ya yabawa kotu kan tsayawa a kan gaskiya ba tare da nuna son kai wajen  yanke hukuncin ba, tare da taya Smart Adeyemi murnar samun nasara.

Ga abinda zance yake cewa: Duk da abubuwan da aka yita fadi game da hukuncin kotun zabe, na cewa ba daidai bane, sai ga shi kuma a yau kotun daukaka kara ta sake tabbatar da wannan hukuncin kamar yadda yake. Ina taya Smart Adeyemi murnar samun wannan nasarar a kotun daukaka kara.

Gaskiyace  tayi halinta a wannan hukuncin , aikin gama ya riga ya gama yanzu kam cewar Yahaya Bello.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More