Yajin aikin ma’aikatan lafiya ba ya kan ka’ida – Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana yajin aikin da gamayyar kungiyar ma’aikatan lafiya ta Joint Health Sector Unions (JOHESU) ta fara a yau Litinin a matsayin “karya doka”.

Sannan gwamnatin ta ce “bai dace ba kuma ba abu ne da ya zama dole ba”.

Kamar yadda ministan kwadago da Samar da aikin yi ,Chris Ngige  ya bayyana cikin wata sanarwa da mataimakin kakakin Ma’aikatar kwadago ta Najeriya ya fitar ranar Lahadi.

Mista Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya ta umarci kungiyoyin da ke karkashin JOHESU da kar su ci gaba da yajin aikin.

Inda ya shawarci kungiyoyin da su sake tunani game da yajin aikin “wanda ba ya kan ka’ida ta hanyar fifita mahimmancin lafiyar mutane fiye da komai”.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More