Yan adawa sun dauki hayar yan Boko Haram dan kawo cikas a zabukan 2019

‘Yan adawa sun dauki hayar ‘yan Boko Haram da ‘yan daba don su kawo tangarda  ga zabukan 2019, in ji Lai Muhammad

Gwamnatin tarayya ta yi ikrarin cewa wani sahihin bayanin sirri ya nuna cewa abokan hamayya sun dauki hayar ‘yan Boko Haram da ‘yan daba don kawo cikas ga zabukan 2019, a cewa ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad.

Ya ce; ” kamar yadda kuka sani, daga yanzu cikin kwanaki 27 masu zuwa, ‘yan Najeriya zasu je rumfunan kada kuri’u. Sai dai kuma gwamnatin tarayya na da sahihin bayanin sirri cewa yawan tada tarzoma da ‘yan adawa ke yi na yin barazana ga zaben du-gari na 2019. Kun dai ga irin kyakykyawar tarbar da cincirindon al’umma ke yi wa Muhammadu Buhari a fadin kasa, idan aka kwatanta da tsirarun mutanen da ke halartar train yan adawa.

Yan adawa wadanda sun karaya na kokarin haifar da tarzoma a fadin kasa don kawo nakasu ga zabuka, wanda hakan zai haifar da rudanin kundin tsarin mulki, wanda ka iya haifar da kafa gwamnatin rikon kwarya.”

Lai Muhammad ya kara da cewa; ” muna da sahihan bayanan sirri cewa an dauki hayar yan Boko Haram da ‘yan daba don kai manyan hare-hare da taxa tarzoma a wasu jihohi a fadin kasa.

” Jihohin da suka hada da Adamawa, Bauchi,Borno, Benue, Kano, Kaduna, plateau, Taraba da Zamfara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More