Yan bindiga su kai hari yobe

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya wato jahar Yobe na nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a garin Katarko da ke kusa da garin Damaturu, a kasar ta Najeriya.

Maharan sun dura  garin ne da yammcin na ranar  Laraba 7 watan Nuwamba 2018, inda suka bude wuta, hakan ya sa mutanen garin kokarin tsira da rayukansu wajen shiga daji.

Wani mutum da ya tsere cikin daji tare da iyalansa, ya shaidawa manema labarai cewa tun yammacin lokacin da  maharan suka fara  harbe-harbe suka gudu daji tare jami’an tsaro dan tsira da rayukan su.

“Mata da kananan yara sun firgita matuka inda suke cikin tashin hankalin rashin sanin abinda ke faruwa ga ‘yan uwa da ke cikin garin,” in ji shi.

Sai dai har  yanzu ba a san ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ko suka zamu raunuka ba a  harin.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.