
Yan bindiga sun kashe kawun Sanata Elisha har gida
96
Normal
0
false
false
false
EN-US
X-NONE
X-NONE
/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}
Yan bindiga sun kashe kawun Sanata Elisha Abbo, sannan kuma sun yi garkuwa da matar mahaifinsa a ranar Asabar 13 ga watan Yuli.
Sanata Abbo, wanda shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta Arewa ya shaida wa BBC cewa dan uwansa ne ya kirashi ya shaida masa abin da ya faru.
Sanatan ya ce, yan bindigar sun je gidan nashi ne tsakinin 12:30 na rana zuwa 1:00 na ranar Asabar din dauke da bindiga samfurin AK-47 inda suka dauke matar mahaifin nasa.
Hakan yasa Kanin mahaifisa ya fara kwarmata ihu,jin yayi wannan ihon da yake yasa suka sai suka harbe shi.
Sanata Abbo ya ce ya shaida wa kwamishinan ‘yan sandan jahar yadda lamarin ya faru.
Sai dai ‘yan sandan sun bayyana cewa suna gudanar da bincike domin ganin cewa sun gano masu hannu a cikin wannan harin.