Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Katsina

Rundunar yan sandan jahar ta Katsina, ta ce yan bindiga kimanin 300 ne suka far wa kauyuka uku na Kirtawa da Kinfau da Zamfarawan Madogara da ke yankunan kananan hukumomin Batsari da Safana.

A wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, DSP Gambo Isah ya ce hare-haren da aka kai ranar Asabar, sun yi sandiyyar mutuwar mutane 10, inda kuma aka jikkata mutane 5.

DSP Gambo Isah ya kuma ce ‘yan bindigar sun rika harbin kan mai uwa da wabi inda suka tarwatsa mutanen kauyen.

Sanarwar ta kara da cewa maharan sun cinna wa ababan hawa wuta,bayan sun kora shanun da ba a san adadinsu ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More