Yan bindiga sun yi awun gaba da wasu mutane a Abuja

Rundunar yan sandan babban birnin Najeriya Abuja ta ce tana kokarin kubutar da mutum biyar da wasu ‘yan bindiga suka awun gaba dasu a yankin Gwagwalada.

Mai magana da yawun runudnar yan sanda babban birnin, Anjuguri Manza ya shaidawa BBC cewa sun kubutar da mutum biyar daga mutanen da yan bindigar suka sace a kauyen mai suna Tungar Maje da ke karamar hukumar Gwagwalada.

A cewar kakakin ‘yan sandan, ‘yan bindigar sun tsallaka da mutane biyar din zuwa cikin jahar Neja mai makwabtaka da Abuja.

“A yayin mummunar musayar wutar da aka yi da yan bindigar, yan sanda sun samu nasarar ceto mutum biyar daga wadanda aka yi garkuwar da su,” in ji Anjuguri Manza.

Wasu mazauna garin sun shaida wa da BBC faruwar lamarin inda suka ce tabbatar da cewa yan bindigar sun tafi da wasu daga cikinsu.

Adamu Tanko mazaunin Tungar Maje ne ya kuma ce maharan sun shiga garin ne da misalin karfe sha biyu na tsakar daren Laraba, inda suka dinga harbe-harbe da bindiga.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More