Yan bindiga sun kashe dan majlisar Bauchi kuma suka yi awun gaba da matansa da yar’sa

 Wasu yan bindiga da ba tantance ba, sun kashe majalisar jahar Bauchi mai wakiltar mazabar Baraza Dass kuma suka sace matansa tare diyar sa mai shekara daya.

Rahotanni sun ce Mataimakin Sufritandan yan Sanda, DSP  Ahmed Wakili na Bauchi  ya tabbatar da rasuwar   Honarabul Musa  Mante Baraza wanda yan bindiga suka kashe shi a dare ranar Alhamis a gidan sa dake Dass.

Ba a tantance su waye suka aikata aika-aikan ba, amma an umarcin tawagar yan’sanda don su gudanar da bincike na gaggawa don gano yan bindigan. Inji Ahmed Wakili.

Idan ba a manta ba, Honarabul Musa Mante yana daga cikin yan majalisar da aka bayyana sun kamu da annobar Coronavirus.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More