Yan Majalisa sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sake bude reshen filin jirgin saman Kano na kasa da kasa

Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake bude filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
A zaman da aka yi a ranar Laraba, majalisar ta bukaci kwamiti musamman kan COVID –19 da “hanzarta umartar” Hukumar Kula da Tashar Jiragen Sama na Tarayyar Najeriya da ta sanya ka’idojin rigakafin coronavirus gabanin sake bude reshen filin jirgin saman na kasa da kasa.
Majalisar ta kuma bukaci kwamitin harkokin jiragen sama da ya gana da ministan jiraje,Hadi Sirika, da , ba tare lokaci ba, ya amince da lokacin da za
a sake bude reshen kasashen duniya na Filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, Kano.
Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Ado – Doguwa; Mataimakin shugaban marasa rinjaye, Toby Okechukwu, da wasu ‘yan majalisar wakilai 32 sun gabatar da kudirin da aka kira da ‘Sake bude reshen kasa da kasa na Filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Kano, don ayyukan Jirgin Kasa da Kasa.’

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More