Yan Majalisar dattawa sun koka kan albashi da alawus din su

Babban bulaliyar majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa wasu abokan aikinsa sun soma yin korafi akan albashinsu  duba da cewa ba haka  suka yi tsammani ba kafin a zabe su.

Kalu, ya bayana hakan ne  a babban birnin tarayya   a Abuja, inda ya sha alwashin bayyana abun da  sanata ke dauka ba da dadewa ba.

Yace ya  karbi albashi sa na watan Yuni kuma ya kasance kasa sosai da abunda mutane ke rubutawa.

Idan minista zai yi tafiya zuwa Legas, da kafafuwansa zai yi tafiya? Abunda kuke kira albashi mai tsoka ne kudaden da muke amfani da shi wajen gudanar da ayyuka a mazaba saboda basu bamu karin kudade.

Kudin ne muke amfani da shi idan zamu yi tafiya zuwa Abia, Legas,ko Kaduna.

Zuwa nan gaba zan bayyana muku,zaku ga cewa korafin da akeyi a kan yan Majalisan Dattawa na banza ne.

Bayan da abokanan aikina  sukayi Korafin hakan, sai yace musu hidima  suka zo yiwa kasarsu a matsayin mu na  sanatoci.

Inda yayi hangen rashen gyautawar  kafofin yada labarai ga yan majalisar dokokin Najeriya.

Duba da cewa, sun  sha fadin cewa dukkan kudade  na  majalisan dokokin kasa ne,  wanda hakan ba gaskiya bane.

Ina kira gareku daku canja ra’ayinku saboda babu albashi mai tsoka kwarai da gaske ban ga ko daya ba.

Idan naga kudin da bai zauna mun a zuciya ba, zanyi magana.

A lokacin da nayi gwamna, jahar ke siya mun abinci, kuma take biyana kudin komai  sabanin yansu a majalisar tarayya.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More