Yan siyasa na da hannu a matsalar tsaron Najeriya – Buratai

Shugaban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi zargin cewa ‘yan siyasa na da hannu a matsalar tsaron kasar ta Najeriya .

Ya yi zargin ne a yayin da yake jawabi ga membobin kwamitin kula da harkokin sojoji na majalisar wakilai ta Najeriya wadanda suka je Maiduguri fadar jahar Borno dan samun bayanai a kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Buratai yace yan siyasan da suka fadi zabe na da hannu wajen karuwar hare-haren ‘yan bindiga da sace mutane a yi garkuwa da su don neman kudin fansa wanda ake fama da shi a shiyyoyin Arewa maso Yammaci da Arewa ta Tsakiya.

Inda ya kara da cewa akwai shaidu masu karfi, sai dai suna taka-tsantsan don kauce wa kuskure .

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More