Yan takarar Zamfara sunyi kira ga hukuma ta gaggauta shiga lamarin su

Gamayyar ‘yan takarar gwamna takwas karkashin inuwar jam’iyyar APC a Jahar Zamfara sun fallasa wani shiri na gwamna Abdul’aziz Yari na son yin amfani da karfin gwamnati wurin shirya makarkashiya da kotu wajen ganin an tilasta wa INEC wurin amsar ‘yan takarar APC tsagin gwamnan.

Gamayyar ‘yan takarar sun yi wannan tonon silili ne a wurin taron manema labarai da suka gudanar shekaran a ranar Litinan 11 ga watan Fabrairu Jahar Kaduna.
Sanata Kabir Garba Marafa, wanda shi ne ya yi jaawabi a madadin gamayyar ‘yan takarar, ya bayyana cewa, wannan shiri na gwamna Yari ya zama rashin sanin ciwon kai.

Tawagar gamayyar ‘yan takarar G8 din sune; Sanata Marafa, Dakta Dauda Lawal (Gamjin Gusau), Malam Ibrahim Wakala, Mahmuda Shinkafi, Mansur Dan-Ali, Aminu Sani Jaji, Abu Magaji, da kuma Mohammed Sagir Hamidu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta haramtawa Jam’iyyar APC tsayar da kowane dan takara a Jahar duba da yanda  Jam’iyyar ta gaza gudanar da zaben fidda  da gwani a iya lokacin da hukumar ta kayyade sakamakon rigingimun na cikin gida da suka addabi Jam’iyyar a lokacin.

Sai dai, kwamitin gudanarwar Jam’iyyar ya cimma yarjejeniyar tsayar da Lawal a matsayin sasanci, wanda a yanzun haka maganan tana gaban kotun daukaka kara.
A ranar Juma’a, Gwamna Yari ya ce, ba za a yi zabe a Jahar ba matsawar babu ‘yan takaran Jam’iyyar APC a cikin zaben, ya nemi hukumar zaben da ta yi aiki da hukuncin da babbar kotun Jahar ta zartas wacce ta tabbatar da cewa, tabbas an gudanar da zaben fidda  da gwani a Jahar.

“A kan haka, ‘yan takaran Takwas suke yin kira ga hukumar shari’a ta kasa da ta gaggauta shiga tsakani a kan lamarin,” in ji Marafa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More