Yan’sanda sun bukaci Alan waka ya gurfanar da kansa

Ranar Litinin 26 ga watan Agusta 2019 Rundunar ‘yan sandar jahar Kano ta aika wa mawaki Aminu Ladan Abubakar, wanda akafi sani da Alan Waka takardar sammaci.

Inda ta bukaci mawakin da ya mika kansa ga ofishin hukumar a ranar Litinin 2 ga watan Satumba 2019, akan wani binciken laifi da hukumar take yi.

Takardar ta bukaci mawakin ya fara mika kansa ga jami’in ofishin da ke kula da harkokin binciken laifuka kan harkokin siyasa.

Yayin da takardar ke dauke da sa hannun mataimakin kwamishinan ‘yan sanda a bangaren binciken laifukan ta’addanci wato DCP Paul Odama.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More