Yansanda sun damke mutum daya cikin wayanda suka kasha mace a jahar Rivers

Rayuka da dana sun salwanta ta sakamakon kashe kashe yan kungiyoyin asiri a jahar Ribas da ke kudancin Najeriya.

Bayan sake dawowar rashin tsaro a jihar Ribas da ke yankin Niger Delta a Najeriya, a baya bayan nan kungiyoyin asiri su na ta cin karensu babu babbaka ta hanyar kisan gilla, wanda hakan yasa wasu kungiyoyin mata a jihar ta Ribas suka gudanar da wani tattaki domin nuna bacin ransu akan wani kisan gilla da aka yi wa wasu ‘yan mata a Otal-Otal a birnin Fatakwal.

Kungiyoyin sun yi tattaki zuwa ofishin rundunar ‘yan sandan jihar ta Ribas da ofishin rundunar tsaro ta farin kaya (wato DSS) da kuma fadar gwamnatin jihar ta Ribas, domin ganin hukumomi sun kara kokari wajan kare rayukan jama’a dama dinbun dukiyoyin jama’a na jihar.

Har ila yau kungiyoyin sun bukaci gwamnati da ta gaggauta janye tambarin mata masu zaman kansu ta dalilin ‘yan matan da aka yi wa kisan gilla ta wannan hanyar.
Daya daga cikin shugabanin masu fafutikar kwato hakkin mata a jihar ta Ribas ta ce wannan kashe kashen ya isa hakanan mata da dama sun rasa rayukan su a jihar ta Ribas, gaskiya kashe kashen ya yi yawa wanda a koda yaushe mata suna mutuwa, kuma ba zamu zura ido ba mata nata mutuwa a matsayinmu na kungiyoyi.

Sannan kungiyoyin sun yi kira ga gwamnatin jihar Ribas da kuma hukumomin tsaro da su kawo karshen wannan matsalar, kuma ya kamata su ringa amfani da kyamarori domin kara inganta sha’anin tsaro a jihar.

VOA ta rawaito cewa shima kwamishinan ‘yan sandan jahar Ribas, Mustapha Dandaura, ya ce mata kimanin tara su ka halaka ta hanyar kasha su a Otal-Otal a jahar ta Ribas a cikin watanni biyu da su ka gabata, kuma rundunarsa ta yi nasarar kama daya daga cikin wadanda suke aikata wannan lafi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da ce sun dauki kwararan matakai a yankin Ogoni da ake kashe kashen, kuma a yau ma har sun kama makamai a wani aiki da suka gudanar na hadin gwiwa tare da sauran jami’an tsaro.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More