Yar Najeriya ta farko da ta fara tuka helikwaftan yaki ta mutu sanadiyyar hadarin mota.

Tolulope Arotile ta rasu ne a ranar Talata bayan gamuwa da hatsarin mota inda ta samu munanan raunuka a Kaduna.

Marigayiyar wace yar asalin jahar Kogi ce, an bayyana cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaki da yan bindiga masu fashin daji a jahar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki.

Babban hafsan sojin sama na Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya ce mutuwar jami’ar babban rashi ce ga rundunar tare da jajantawa iyalanta a madadin dukkanin jami’an rundunar sojojin sama na Najeriya.

Hotuna daga Nigerian Air Force

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More