Yar wata hudu ta kamu da Coronavirus a Kaduna

Gwammnatin jahar Kaduna ta tabbatar da cewa an samu jaririya ‘yar wata hudu cikin karin mutane 20 da suka kamu da annobar cutar ta Covid19 a ranar Juma’a 15 ga watan Mayu 2020.

Sanarwar tace,an yi wa jaririyar gwajin cutar ne bayan an kai ta asibiti bisa matsalar numfashi kuma yanzu haka ana jiran sakamakon gwajin da aka yi wa iyayenta.

Ma’aikatar lafiya a jahar ta ce bincikenta ya nuna cewa mahaifin jaririyar ya je jahar Kano a ‘yan kwanakin da suka wuce.

A wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar ta jahar ta wallafa a shafin ta na Twitter a yau Asabar 16 ga watan Mayu, tace mutane 15 daga cikin sabbin wadanda suka kamun da Coronavirus din ‘yan uwan wani mai dauke da kwayar cutar ne.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More