Yara 27 yan’sanda suka ceto daga gidan marayu na bogi a Arewa  

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta ceto yara 27 daga jahar Kano da Kaduna da ke arewacin kasar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Kano DSP Abdullahi Haruna ya shaida wa BBC cewa sun ceto yara 19 daga wani gidan marayu a jahar Kano wanda ake kira ”Du Merci”.

Inda ya bayyana cewa tare da taimakon hukumar NAPTIP, an ceto wasu yara takwas daga jahar Kaduna a gidan marayun na Du Merci da ke reshen jahar ta Kaduna.

‘Yan sandan sun tabbatar da cewa gidan marayun na bogi ne.

A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan jahar Kano shawara kan jin dadin yara da walwala da kuma dawainiyar mata Hajiya Fatima Abdullahi Dala, ta fitar da cewa gidan marayun ya shafe shekaru 25 yana aiki ba tare da lasisi ba ko sanin gwamnati.

Fatima tayi kira ga jama’ar Kano kan cewa su sa ido domin bayar da rahoto kan irin wadannan wurare da ke aiki ba tare da sanin gwamnati ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More