Yau Juma’a BBC zata bayanna gwarzuwar  Hikayata ta bana

A daren yau Juma’a 25 ga watan Oktoba 2019  BBC zata ta  bayyana Gwarzuwar Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, cikin mata uku.

Matan sune:

Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo

Jamila Babayo

Safiyya Ahmad

Labaran wadannan marubuta ne dai alkalan gasar suka zaba a matsayin wadanda suka cancanci kaiwa wannan mataki.

Abin da ya sa labaran suka yi fice kuwa, a cewar jagorar alkalan Dokta Aliya Adamu, shi ne “Salo”.

Salo

Ta kara da cewa, “Salo dubara ce ta isar da sakonka; to wadannan gajerun labarai, duk da suna gajeru, marubutan sun yi amfani da wani salon a daga hankalin mai sauraro ko mai karatu, kuma su hukunta ko wane tauraro daidai da rawar da ya taka a cikin labara”.

Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta kai wannan matsayi ne da labarinta mai suna “Ba A Yi Komai Ba”.

“Ba A Yi Komai Ba” labari ne a kan Uwani, wata mata da ke haifar ‘ya’ya mata—sakamakon haka mijinta da danginsa suka uzzura mata har dai daga karshe ya sake ta.

Ita kuma Jamila Babayo labarinta mai suna “A Juri Zuwa Rafi” ne ya kai ta wanna matsayi. Labarin dai na wata yarinya ce Aisha wadda wani mawadaci a unguwarsu ya yi mata fyade, sannan dangina gaba daya suka nemi a rufe maganar, amma mahaifiyarta ta ce sai ta kwato mata hakkinta.

Labarin “Maraici” kuwa, wanda da shi Safiyya Ahmad ta samu kaiwa wannan matsayi, yana magana ne a kan Karima—wata yarinya da ta taso a gidan marayu, daga baya ta samu uwar riko wadda ta uarar da ita, amma zaman auren ya gagara saboda wulakancin da take fuskanta sakamakon kallon da ake yi mata na mara asali.

Labarai fiye da 300

Wadanda suka yi alkalancin gasar dai su ne Dokta Aliya Adamu, malama a Jami’ar Jihar Sokoto, kuma kwararriya a kan Tarihin Adabi a Nazarin Harshen Hausa, da Hajiya Bilkisu Salisu Ahmad, fitacciyar marubuciyar nan da masu sha’awar rubuce-rubucenta suke kiran ta Aunty Bilki, da kuma Malama Bilkisu Yusuf Ali, marubuciya kuma mai nazari a kan adabin Hausa, kuma malama a Jami’ar Al-Qalam da ke Katsina, a Najeriya.

Wadannan alkalan sun zabo labaran uku ne daga cikin 25 din da aka tura masu.

Kafin nan sai da aka fitar da labarai 30 daga cikin sama da 300 da aka shigar a bana.

Kuma ko wanne labari daga cikin 30 sai da ya cika ka’idojin shiga gasar, wadanda suka hada da kasasncewa kagagge, da kasancewa marubuciyar ce ta rubuta shi, da kauce wa batanci da zagi, da amfani da ingantacciyar Hausa, da sauransu.

A cewar Malama Bilkisu Yusuf Ali, “Za ki ga wani a cikin ka’idojin ne yake faduwa—labarin da a ce ya bi wadannan ka’idojin dakidaki, da sai ki ga watakila shi ne zai yi nasara”.

Bayan nan kuma alkalan sun yi amfani da wadansu ma’aunai don tantance labaran.

Wadannan ma’aunai dai sun hada da salo, da hawa, da sauka, da rike mai karatu, da farkon labari, da sauransu.

Gwarzuwa ta hudu

Duk wadda ta yi nasara ita ce za ta zama ta hudu a jerin gwarazan gasar, wacce aka fara a shekarar 2016, kuma za ta karbi kyautar kudi dala 2,000 da lambar yabo.

Marubuciyar da ta zo ta biyu kuma za ta karbi kyautar kudi dala 1,000 da lambar yabo, sannan wadda ta yi ta uku za a ba ta kudi dala 500 da lambar yabo.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More