Yau take ranar Hausawa ta Duniya ko wanda bahaushe ya fito ya tufa albarkacin bakin sa

Masu ta’amali da kafafen sadarwa na zamani a harshen Hausa sun fara wani babban yunkuri na ayyana ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara ta zama ranar Hausa ta duniya. Masana sun bayyana cewa, ayana wata rana don tunawa da wani abu da ya faru, ba sabon abu ba ne. Sai dai a irin wannan ranar ana ayyana ta ne danagane da wani abu da ya da ya faru na tarihi da ke da dangantaka da wannan ranar.

Saboda haka ne ma Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana wasu ranaku wadanda ake tunawa da wasu abubuwa da suka faru a irin wadannan ranaku. Misali akwai ranar tunawa da masu cutar kanjamau ko masu tarin fuka da sauran wasu muhimman ranaku. Haka kuma, akwai ranaku irin su ranar mulkin kai da sauransu, a daidaikum mutane kuma a kan tuna da ranar haihuwa da makamantan irin wadannan ranaku. Bisa irin wannan tunanin wasu masu kishin harshen Hausa suke ganin yana da matukar muhimmanci su gabatar da wannan bukata ta su ta neman ayyana ranar 26, ga watan Agusta ta kowace shekara ta zama ranar Hausa ta duniya, ranar da masana da masu sha’awar harshen Hausa za su dinga gabatar da bayanai a kan abubuwan da suka shafi harshen, kamar na ci gabansa ko manyan kalubalen da ke tattare da shi. Bisa wannan ne wakilinmu ya tattauna da wasu masana irin su Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza da ke Sashin Nazarin Harsuna da Al’adu na jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau, da Dakta Shu’aibu Hassan na Sashin Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka da ke jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. A bangaren yada labarai kuma wakilin na mu ya tattauna da jagoran shirye-shirye na gidan rediyon FM na jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya, Malam Aliyu Abdulrahman. Haka kuma ya tattauna da shahararren malamin makaranta kuma shugaban Cibiyar koyar ilimin manya da ke Shahuci Kano, Alhaji Garba Baban Ladi Satatima dangane da wannan rana.

Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza ya ce, wannan yunkuri yana da matukar muhimmanci, kuma yakamata a yabawa masu wannan kokari, domin sun dada fito da matsayin harshen Hausa da kuma kokarin kara masa tagomashi. Harshen Hausa, harshe ne da ya samu karbuwa a duniya, don haka, bisa wata kididdiga da aka yi kwanan nan, ta nuna cewa harshen Hausa shi ne harshe na goma sha daya a duniya. Saboda haka harshe ne wanda za a iya koyar ilimin kimiyya da fasaha da kowane irin ilimi da shi. Saboda haka, shawarata a nan, a samu masana da magabata a tattauna dangane da tsayar da ranar da ta fi dacewa, wato a samu wata rana wadda idan aka ambata ta kowane Bahaushe zai ji an yi masa susa inda yake yi masa kaikayi. Kamar a ce ranar da Farfesa Galadanci ya Ra rasu ko ranar da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya ya riga mu gidan gasiya ko ranar wani shahararren mawaki a kasar Hausa ya rasu ko ranar da Daular Daura ko Gobir ta kafu, da dai makamantan irin wadannan abubuwa, wadanda dalibai da Hausa za su ji ayyana wannan rana za a tuna musu da faruwar wani muhimmin abu  da ke da dangantaka da harshen Hausa. Duk da haka na jinjinawa wadanda suka fara wannan tunani, kuma ko da an sauya wannan rana to sun shiga cikin tarihi kuma ya kamata a karrama su. Shi ma a nasa tsokacin Dakta Shu’aibu Hassan, na jami’ar Ahmadu Bello, ya bayyana cewa, lallai wannan yunkuri ne mai kyau, sai dai kamar yadda Farfesa Bunza ya fada a baya, yakamata masana da manazarta harshen Hausa su tattauna yadda za su samar da wata muhimmiyar rana da wani abin tarihi a harshen Hausa ya faru. Sai a ayyanata ta zama ranar Hausa ta duniya. Amma duk da haka wannan yunkuri yakamata ya zaburar da masanan ne wajen fito da ita wannan rana wadda kowa zai amince da cewa ta dace da ta zama ranar Hausa ta duniya. Akwai ranaku daban-daban da aka ayyana domin tunawa da wani abu, to amma za ka samu dukkan wadannan ranaku na da tarihi na dangantaka da abin da ake tunawa da shi a wannan rana. Saboda haka, wannan, motsi da wasu suka fara yi kamar jawo hankali ne na tunani a kan wannan rana, kuma sun cancanci yabo, domin kuwa sun taso da wani abu da za tattauna a kansa kuma da fatan nan gaba kadan a samu cikakkiyar matsaya yadda ranar za ta samu karbuwa kuma ta shiga cikin jerin ranakun da aka amince da su wanda da zarar ranar ta zo za gudanar da wasu hidimomi da za su kara fito da gudummowar harshen da yaduwarsa da kuma kalubalen da yake fuskanta, har ma da hanyoyin da za a bi wajen tunkarar wadannan kalubale.

 

Malam Aliyu Abdulrahman, danjarida kuma shugaban Sashen shirye-shirye na gidan rediyon jami’ar Ahmadu Bello da ke Samarun Zariya, ya bayyana gamsuwarsa da wannan kokari na ayyana wannan rana a matsayin ranar Hausa ta duniya. Ta fuskar yada labarai, harshen Hausa, ya yi fintinkau ga wasu harsuna masu yawa da ke fadin duniyar nan, domin kuwa bisa wannan shara ce ma da ya yi aka fara wannan tunani na ayyana wata rana da za ta zama ranar Hausa ta duniya. Kusan babu wata kasa da ke jin kanta a duniya kuma take watsa shirye-shiryenta na rediyo ga duniya da ba ta gabatar da labarai ko ma wasu shirye-shirye cikin harshen Hausa. Tun shekaru aru-aru muke jin Sashin Hausa na BBC da na Amurka da na Jamus da Akahira daga baya kuma aka samu Sashin Hausa na gidan rediyon kasar Sin da Iran da Ghana da DW da ma sauran wasu kasashe duniya. Sannan kuma idan ka dawo cikin gida Nijeriya akwai gidajen rediyo masu yawa da ke gabatar da labarai da shirye-shirye cikin harshe Hausa. Haka ta fuskar jaridu nan ma an samu ci gaba sosai wajen samun labarai da dumi-duminsu domin kuwa a halin yanzu ana kafada-da-kafa da jaridun Ingilishi musamman yanzu da aka samu jaridar Hausa mai fitowa kullum,kamar OAKTV HAUSA, LEADERSHIP A YAUda dai sauran su. Don haka nake ganin wannan kokari na ayyana wannan rana ta 26 ga watan agusta na kowace shekara a matsayin ranar Hausa ta duniya, tamkar a ce sara ne ya zo a kan gaba.

Shi kuwa shararren malamin nan da ya shafe sama da shekara hamsin yana koyar da ilimin manya a jihar Kano Dakta Garba Baban Ladi Satatima, ya bayyana cewa, harshen Hausa, harshe ne da ke ci gaba da bunkasa a duniya. Dalilai da yawa suka sa wannan harshe na Hausa zai ci gaba da bunkasa kuma ma zai ci gaba da hadiye wasu kananan kabilu.

Da farko Hausawa mutane ne da ke karbar baki daga kowace kabila na ciki da wajen kasar nan, kuma sukan yi hulda da su kamar yadda za su yi hulda da ‘yan gida. Hausawa na da al’ada ta karrama dukkan wani bako da ya zo wajensa, don haka ne ma yake cewa, “Bakonka Annabinka” wannan karrama da Bahaushe ke yi wa bakonsa ta sa, su bakin kan sakankance da Hausawan su yi hulda tare da su cikin walwala da sakin jiki, wanda hakan ta sa suke kokarin koyon harshensu, su kuma suke koya musu. Saboda haka, da zarar Bahaushe ya yi hulda da wani kabila cikin sauki yakan koya masa harshen Hausa. Wani abu kuma da ke kara habaka harshen kamar yadda toshon Malamin makarantar ya fada shi ne, saukin da harshen ke da shi wajen koyo, harshen Hausa ba shi da wasu kwayoyin sauti  ko kalmomi da suka bayar da wahala sosai wajen furta su ga wanda ba dan asalin harshen ba, musamman idan ka kwatanta shi da harshe irin na Ibo. A nan ma saukin harshen ya taimakawa wajen hadiye yaren wadansu kananan kabilu da suka yi doguwar hulda da Hausawa. Baya ga wannan, akwai wasu kabilun da ake musu zargi da munafunci ga wanda ya matso kusa da su wanda ba dan kabilarsu ba, saboda haka ake ganin ba sa son sake jiki su koyar da harshen nasu, domin in har wancan zargin ya tabbata, su samu sukunin baje hajarsu ta yin munafunci ga wanda ba ya jin abin da suke cewa. Shi kuwa Bahaushe ya tsira daga wannan zargin, don haka, da zarar wani kabila ya fara hulda da shi, kokarinsa ya koya masa harshen nasa, wannan ma ana ganin yana daga cikin abin ya bunkasa harshen Hausa a duniya. Haka kuma, harshen ya samu albarkacin ilimi.  Zurfafa bincike a harshen da fadada shi zuwa fannonin ilimi daban-daban ya taimaka wajen karawa harshen tagomashi da kuma fito da wasu sababbin kalmomi da suka taimaka wajen bunkasar harshen. Huldar kasuwanci da neman ilimin addini da tafiyen-tafiyen da Bahaushe ke yi su ma sun bayar da gudummowa wajen isar da harshen ga dimbin al’ummar da wasu ma ba su taba takowa Nijeriya ko Nijar ba. Saboda haka, nake ganin dacewar wannan yunkuri na ayyana wannan rana ta 26, ga watan Agusta a matsayin ranar Hausa ta duniya, yadda magabata da masana da ‘yan asalin harshen za su fito su yayata irin wannan bajinta da Hausawa da harshen Hausa ke da su, wadanda suka mayar da shi cikin sahun gaba a cikin jerin harsunan duniya.

Cc leadership a yau

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More