Yaya kuke so ta kaya yau a kotun koli tsakanin shugaba Buhari da Atiku?

Alkalan Kotun kolin Najeriya za su fara sauraron karar da Atiku Abubakar ya daukaka a game da shari’ar zaben shugaban kasa.Yayin da dan takarar na babar jam’iyyar adawa wato PDP yake kalubalantar nasarar ta jam’iyyar APC.
 
Alkalan Atiku Abubakar na ikirarin cewar, ba shugaba Buhari na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da aka gudanar na ranar Asabar 23 ga watan Fubrairun 2019.
Kotun farko ta yi watsi da karar, da Atiku Abubakar ya ya shigar a gaban kotun sauraron korafin zabe. Sai dai Atiku ya daukaka kara zuwa babbar kotun kasar da nufin ganin an rusa nasarar da shugaba Buhari ya samu.
A yau Laraba 30 ga Watan Oktoba 2019 ake shirin fara shari’ar, sai dai har yanzu babu wanda ya san Alkalan da aka zaba a kotun kolin domin su karbi korafin da Lauyoyin Atiku su ka shigar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More