Yin watsi da maganar kirkirar sabbin marautu a Kano zai fi zama alkairi – Aminu Daurawa

Menene ra’ayin ku game da hakan?

Yin watsi  maganar kirkirar sabbin masarautu a Kano a ganin mu shi ne zai zama mafi alkairi ga al’ummar jahar Kano cewar fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya Sheikh Aminu Daurawa.

Daurawa ya  bukaci gwamnatin jahar Kano da ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin mutanen jahar gamada al’amarin kirkirar sabbin masarautun a Kano.

A tattaunawar da malamin yayi da Hausa RFI, ya ce suna ganin rashin kirkirar sabbin masarautun shi zai fi alkairi, don kauce wa rabuwar  kawunan al’umma.

Bayan an karanta bukatar kashi na uku, a ranar Alhamis majalisar ta amince da hakan ya zamo doka a jihar. biyo bayan gabatar da kudirin da Ganduje ya kara yi a gaban majalisar a ranar Litinin da ta gabata,duba da  cewa babbar kotun jahar ta soke sabbin masarautun tare da dakatar da sarakunan da gwamnan Ganduje ya nada.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Labaran Abdul-Madari ya ce, manufar kirkirar sabbin masarautun ita ce bunkasa ci gaba a fadin jahar kuma sun dau matakin domin talakawa ne.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More