Za a fara haska Mariya ranar Sallah a cinema

Za a fara haska fitaccen fim din mai suna  Mariya a ranar Sallah a sinima inda za a haska shirin harna tsawon   mako biyu a Ado Bayero Mall  dake Kano kafin ya fita zuwa wasu jihohin.

Fim din da  aka kosa a ga fitowar sa, yana cikin fina-finan da ake yawan tattaunawa a kansa duk da cewa bai riga ya fito ba.

Fim ya canja akalarsa ne zuwa wani fage da ba’a  saba ganin irinsa ba a masana’antar Kannywood, ta yadda fim ya mayar da hankali kan auri.

Daga cikin wadanda suka baje kolinsu a fim akwai Sarki Ali Nuhu da Maryam Yahaya wadda ta fito a matsayin Mariya da Umar M Shariff da sauransu. Kuma Abubakar Bashir Maishadda ne jagoran shirin.

You might also like More from author

Comments are closed.