Za’ a gudanar da aikin hajji a wannan shekarar ta 2020- Saudiyya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta ce mazauna kasar ne kadai – cikinsu har da ‘yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta – za a bari su gabatar aikin Hajjin bana.

A  sanarwa da ma’aikatar aikin Hajji kasar ta fitar  na  cewa, sun dauki mataki ne bisa la’akari da yadda cutar Coronavirus ta yadu zuwa kasahe sama da 180 a fadin duniya, da kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar da wadanda ke dauke da ita da suka kai miliyan bakwai a fadin duniya.

Ga rashin riga-kafin annobar da ake fama da ita a duniya da kuma bukatar tabbatar da tazara tsakanin mutane da hana taron jama’a duka wadannan na daga cikin dalilan da ya sa aka soke Umara a bana, in ji sanarwar.

Za a bayar da tazara yayin gudanar da aikin Hajjin kuma za a gudanar da shi kan doron koyarwar addinin musulunci kamar yadda aka saba.

Saudiyya ta dauki wannan matakin ne dan tabbatar da aminci ga duk wani mahajjaci da ke kasarta har sai sun koma kasashensu na ainihi.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More