Za a iya tura masu hidimar kasa yaki idan bukatar hakan ta taso- Babban Daraktan NYSC

Darakta-Janar na hukumar bautar kasa ta NYSC, Brig.Gen Shuaibu Ibrahim, ya ce mambobin bautar kasar wani bangare ne na manufofin tsaron kasa na Najeriya kuma za a iya hada kansu don yaki idan akwai bukatar hakan.
Ibrahim ya fadi haka ne a shirin ‘Sunrise Daily’ na gidan Talabijin din Channels a ranar Laraba yayin da yake mayar da martani game da koma baya ga shirin NYSC wanda ya zama tilas ga duk ‘yan Nijeriya da suka kammala karatu kafin su cika shekaru 30.
Shugaban NYSC din ya ce, “mambobin bautar kasar suna nan a ajiye. Suna daga cikin manufofin tsaron kasa na wannan kasar. Don haka, inda akwai babban yaƙi, membobinmu masu bautar ƙasa suna da ilimi, suna da ilimi kuma ana iya horar da su…
“Za ku iya tunanin cikin gajeren makonni uku a sansanin su, ana horas da mambobin bautar kasar. Suna kama da sojoji. Ka ga ‘yan bautar kasa mata suna busa kaho, suna wasa da kungiyar sojoji.
“Don haka, in ba don ilimin ba, a ina za ku tattara irin wadannan matasa ‘yan Najeriya don horar da su cikin hanzari don sanya mafi kyawun abin da suka yi wa kasar? Don haka, membobin bautar kasan suna nan a kasa . Hakanan suna daga cikin manufofin tsaron kasa.”
Ya ce NYSC ta damu da tsaron ‘yan yi wa kasa hidimar don haka ne ya sa aka ba su shawarar kada su rika yawo da daddare.
Ibrahim ya ce NYSC ta zama mai muhimmanci fiye da kowane lokaci a yayin da ake ta samun karuwar kiraye-kirayen ballewa daga kasar.
Shugaban NYSC din ya bayyana cewa ya shawarci masu yi wa kasa hidiman da kada su yi tafiya a wajen jihar ko kasar ba tare da izinin mai kula da jihar ba.
Ya kara da cewa an yi kira ga mambobin kungiyar da kada su yi tafiya bayan karfe 6 na yamma kuma suna da damar yin bacci a kowane masaukin masu bautar yayin tafiya.
Ibrahim ya ce mambobin bautar kasar sun taka rawar gani wajen ilimantar da yara a sansanonin ‘Yan Gudun Hijira.
Shugaban na NYSC ya ci gaba da cewa rashin tsaro a kasar bai isa ya kawar da shirin ba, ya kara da cewa har zuwa yau, kashi 75 na masu bautar kasa suna ci gaba da aiki a yankunan karkara a duk fadin kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More