Za ‘a kafa wata sabuwar rundunar da zata maye gurbin SARS

Menene ra’ayinku game da wannan batun?

Babban sufeton yan’sandan Najeriya Muhammadu Adamu yace za a samar da dandali yadda shuwagabannin  na yan sandan zasu yi aiki da jama’a a  dukkan mataikai don sa ido a kan ayyukan  ‘yansandan.

Matakin soke rudunar  ta SARS bai yi wa wasu al’umma dadi ba, wanda suke ganin hakkan ka iya haifar da babbar gibi a harkokin na tsaro, yayin da wasu kuma ke cigaban da gudanar da zanga-zangar ta Endsars  a fadin kasar.

Grop captain Sadik Garba Shehu  wanda shima masanin tsaro ne , ya bayyana cewa, a maimakon a  soke  rudunar ta SARS kamata yayi a mata garambawul saboda mutanen da suke  aikin har yanzu su ‘yansanda ne. Kamar yadda Muryar Amurka ta rawaito ya yace.

#OakTV #OakTVHausa
#OakTVOnline

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More