Za a yi wa Buhari da Osinbajo allurar rigakafin COVID-19 a ranar Asabar

Za a yi wa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, allurar rigakafin Covid-19 ta AstraZeneca / Oxford a ranar Asabar.
Daraktan zartarwa na Hukumar Bunkasa Kiwon Lafiya a matakin farko, Dokta Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da manema labarai a gidan Gwamnatin da aka yi a Abuja ranar Alhamis.
A cewarsa, atisayen zai kara wa ‘yan Najeriya karfin gwiwa na karbar kimanin allurai miliyan hudu na AstraZeneca / Oxford na rigakafin COVID – 19 da aka shigo da su kasar a wannan makon.
Shuaib ya ce, “Mataki na gaba a shirin allurar rigakafin ganin cewa yanzu mun karbi alluran riga-kafi ne wanda za a fara a Babban Asibitin Kasa gobe (Juma’a) . Lokacin da aka tsara don ƙaddamarwa shine 10 na safe. Shugaban Kwamitin Tsaro na Shugaban kasa kan COVID – 19, (Boss Mustapha) ne zai gudanar da kaddamarwar.
“Shirin shi ne a yiwa ma’aikatan lafiya na gaba wadanda ke aiki a cibiyar kula da lafiya ta Asibitin Kasa, wadanda za su kasance mutanen farko kamar yadda muka sanar cewa ma’aikatan lafiya na mataki na gaba za su kasance mutanen farko da za su fara yin allurar.
“Bayan haka, shirin shi ne a yi wa Shugaban kasa, Mataimakin Shugaban kasa da manyan jami’an gwamnati allurar rigakafi a ranar Asabar. Bugu da ƙari, muna fata cewa lokacin da ‘yan Nijeriya suka ga shugabanni irin su Shugaba da Mataimakin Shugaban anyi musu rigakafin; hakan zai kara musu kwarin gwiwa game da sahihancin allurar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More