Za mu ci gaba da binciken Ganduje – Majalisar Kano

kwamitin majalisar dokokin jahar Kano wanda ta ke  gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa gwamna Ganduje na karbar cin hancin miliyoyin dala gurin wayanda ba’a baiyana sub a, ya ce zai ci gaba da aikinsa, duk da cewar kotu ta bada umarnin dakatar da binciken.

Bayan kotun ta  jahar Kano ta bukaci kwamitin da ta dakatar da binciken, bayan wata kungiyar lauyoyi masu rajin kare demokaradiyya ta shigar da kara tana zargin cewa kwamitin majalisar dokokin ba shi da hurumin binciken gwamnan

Sai da kuma Shugaban kwamitin Hon Bappa Babba Dan-Agundi ya shaidawa ma nema labarai cewa, a fahimtar majalisarsu kwamitin zai ci gaba da gudanar da bincikensa kamar yadda ya tsara don ba cewa aka yi a daina aiki ba.

Bappa Babba Dan Agundi, ya ce kwamitin zai kuma je kotu domin ya girmamata saboda mutanen da ke amajalisar su ne yakamata su kare martaba da mutuncin kotun.

Shugaban kwamitin binciken ya ce, a abinda aka ba su, kotu ba ta ce su daina aikin da suke ba, amma kuma idan har suka je kotun ta kuma ce su daina binciken da suke yi, ai dole su girmama kotu.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.