Za’a ci ba da garkame iyakokin Najeriya dan ci gaban tattalin arziki Najeriya

Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Hamid Ali, ya bayyana cewa, iyakokin Najeriya za su ci gaba da kasancewa garkame har sai lokacin da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya suka dena baiwa masu fasa-kwauri shigo da kayan da kasar ta haramta shigowa dasu.
 
Shugaban hukumar ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ziyararci Maigatari, da ke jahar Jigawa wanda yake kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.
 
Ya ce Najeriya ba za ta taba yin shiru ta zuba ido wajen kyale wadansu kasashen su kassara tattalin arzikin ta kasar ta Najeriya ba.
 
Ali ya shaida wa yan jarida cewa kasashen da suka hada makwabtaka da Najeriya sune kanwa uwar gami wajen marawa masu safarar iri-iren wadannan kaya da suka haramta shigo dasu tare da cewa kuma kasashen sun san yadda fasa-kwaurin irin wadannan kayayyakin zai yi ga ci gaban Najeriya.
 
 
Ya ce duk da yadda suka dauki kwararan matakai, amma kuma kofar tattauna a kan lamarin a bude take wajen samun fahimtar juna da sabuwar yarjejeniyar da za ta ba manufofin tsarin tattalin arzikin Najeriya mutunci da kuma kima.
Menene ra’ayin ku game da haka?

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More