Za’a ci tarar 5000 ga dan adaidaitan da aka kama ya hada Mace da Namiji a Kano

Menene ra’ayin ku game da hakan?

Gwamnatin na jahar Kano da sake dawo da dokar ta hana  hada mace da namiji a cikin keke napep  wato Adaidaita sahu,  bias dalilin ta na  habbaka koyarwar addinin musulunci na kare mutunci da kimar mata a jahar, dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2020.

Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta fitar da sanarwar cewa, duk wani mai adaidaita sahu da aka kama yana daukan mata da maza a lokaci guda zai fuskanci hukuncin bulala 10 ko a dakatar da shi daga aiki na tsawon watanni 6.

Shugaban Hisbah Harun Ibn-Sina ya shaidawa Premium Times cewa za a bawa wadanda aka samu da laifin zabin biyan tarar N5,000 idan kuma ba haka za su fuskanci hukunci daidai da irin laifin da suka aikata.

Kwamanda na Hisabah ya ce duk wani direban adaidaita sahu da aka kama yana dauke da mace da namiji  a lokaci guda ya aikata laifi a karkashin dokar tuki na jahar Kano da aka yi wa kwaskwarima a 2005.

Da zarar an kama direban, za a garzaya da shi kotun tafi da gidan ka, kotun majistare ko kuma kotun Shari’ah. Ibn Sina ya ce dokar ba ta shafi ma’aurata,  kananan yara da kuma ‘yan gida daya ba. Ya ce an dauki matakai da suka dace domin ganin samun nasarar aiwatar da dokar tare da goyon bayan hukumar kiyaye cinkoson ababen hawa ta Kano wato KAROTA da sauran hukumomi.

Sai wani lauya mazaunin Kano  mai suna Rabiu Rijiyar, Lemu ya ce dokar da Hukumar ta Hisbah ta fitar zai kawo matsala tsakanin masu adaidaita sahu, fasinjoji da kuma jami’an tsaro a jahar, inda ya kara da cewar idan har  Hisbah ba za ta iya gabatar da rubutaccen doka da ke bayani kan bulala ko dakatarwar na watanni shida ba tare da cin tarar N5,000 kan hada mace da namiji to dokar ba za tayi aiki ba don ta ci karo da sashi na 36 na kudin tsarin mulkin kasa ta 1999.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More