Za’a cigaba da tsare Adoke na tsawon kwanaki 14 dan gudanar da bincike.

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa wato  EFCC ta samu daman cigaba da tsare tsohon ministan sharia Mohammad Bello Adoke, a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Wata babbar kotun Abuja ce ta baiwa EFCC izinin cigaba da tsare Bello Adoke na tsawon kwanaki 14 domin gudanar da cikakken bincike a kansa, sakamakon zarginsa da take yi da hannu cikin aikata laifin rashawa.

A ranar Alhamis ne jami’an Yansandan kasa da kasa watau INTERPOL ta taso keyar Adoke zuwa gida Najeriya bayan kama shi da ta yi a kasar Dubai tsawon makonni 5 da suka gabata, INTERPOL ta kama shi bisa umarnin kasar Dubai, bayan gwamnatin Najeriya da Dubai sun tattauna batun.

EFCC na tuhumar Adoke ne da zargin hannu cikin badakalar sayar da rijiyar hakan danyen mai a OPL 245 ga kamfanonin Shell da ENI, don haka Alkalin kotun, mai sharia Othman Musa ya bayar da wannan umarni ga EFCC domin ta gudanar da bincike yadda ya kamata.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More