Zabe Kano: Kotu ta bada ummarnin damko wayanda suka kaiwa INEC hari

Kotun sauraron karrar zaben gwamnan Kano, karkashin jagorancin Justice Halima Shamaki ta bayar da umurnin kamo wadanda ake zargi da kaiwa wata ma’aikaciyar INEC, Halima Sambo Hassan da ta bayar da shaida a kan shari’ar zaben gwamnan Kano da ke gaban kotun.
 
Alkalin ta bayyana harin da aka kaiwa Hassan a matsayin ‘gidadanci’ kuma ta bawa hukumomin tsaro umurnin fara bincike kan lamarin. Ta kuma bukaci jami’an tsaron su binciko wadanda suka kai harin tare da hukunta su kamar yadda doka ya tanada.
 
Yayin da Justice Shamaki ta bayyana cewar kotun ba za ta amince da duk wani rashin da’a daga magoya bayan jam’iyyun biyun da suka shigar da karar ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More