Zaben 2019: INEC ta koka bisa jam’iyyin siyasa kan kin bayyana abun da suka kashi a zaben

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta bayyana cewa, jam’iyya daya ce ta bayyana rahotonta dangane da kudaden  da ta kashe a zaben da aka gudanar na 2019.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana hakan ne a  taron nazarin zaben 2019 tare da jam’iyyun siyasa da aka gudanar  a ranar Litinin1 ga watan Yuli 2019 a babban birnin tarayya Abuja.

Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, dan takarar shugaban kasa daya ne kawai ya kawo bayanan kudaden da ya kashe a zaben, inda ya nuna cewa  har yanzu babu jam’iyyar siyasar da ta bin dokar zaben wanda  ke nuna cewa,dole ne jam’iyyun siyasa su bayyana kudaden da suka samu daga daidaikun mutane da kuma kungiyoyi dangane da zaben.

A karshe ya bayyana cewar ya kamata jam’iyyun siyasar su bi dokar zaben kafin wa’adin dokar ya kare.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More