Zaben 2019: Manyan sanatocin da suka rasa kujerunsu

A ranar 23 ga watan Fabrairu ne aka yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar Tarayya a Najeriya.
Bayan sama da sa’a 48 sakamakon zaben ‘yan majalisa ya fara fitowa sai aka ga wasu daga cikin manyan sanatocin da aka sani sun sha kaye, al’amarin da ya zo wa mutane da dama da mamaki.
Bukola Saraki
Shi ne shugaban majalisar dattijan Najeriya, wanda ya haye kujerar a 2015 a karkashin jam’iyyar APC. Sai dai daga baya ya samu sabani da Shugaba Buhari inda har ya bar jam’iyyar zuwa PDP.
Tun a wancan lokacin ‘yan Najeriya da dama suka fara sharhin cewa ga alama ‘faduwar daular Saraki ce ta zo a siyasance.”
Mutane sun yi ta sharhi kan faduwar shugaban majalisar ganin cewa shi ne mutum na uku mafi girman mukami a Najeriya., kuma shi ne babban darakta na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Duk da cewa ‘yan gidan Saraki sun dade suna mulkin jihar Kwara tun daga kan mahaifinsa zuwa kansa, a bana an samu rabuwar kai tun daga cikin gidansu ma, inda kanwarsa Gbemisola Ruqayyah Saraki ma ta raba gari da shi.
Sannan duk da cewa gwamnan jiharsa Abdulfatah Ahmed yaronsa ne, hakan bai hana shi faduwa a zaben ba.
Yanzu dai ‘yan Najeriya za su zura ido don ganin yadda za ta kayawa Saraki cikin shekara hudu masu zuwa, ganin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta PDP Atiku Abubakar ma bai kai labari, ballantana a sa masa ran samun mukamin da zai iya share masa hawaye.
Shehu Sani
Shehu Sani fitaccen Sanata ne na Kaduna Ta Tsakiya da ya je majalisa a 2015 karkashin jam’iyyar APC.
Jim kadan bayan zaben 2015 ne sai Sanata Sani ya fara samun matsala da gwamnan Kaduna Nasir el-Rufa’i wanda a da suke dasawa.
A watan Mayun 2018 ne da rashin jituwar tasu ta yi kamari sai Sanata Sani ya bar APC zuwa PRP. Ya kuma nemi kujerar sanatan Kaduna Ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar PRP a zabukan baya-bayan nan na 2019, sai dai ya sha kaye a hannun dan takarar APC, Uba Sani.
George Akume
Akume tsohon gwamnan jihar Binuwai ne kuma Sanata mai wakiltar Binuwai ta Yamma.
Jam’iyyar PDP ke mulkin jiharsa a halin yanzu bayan da gwamnan jihar ya sauya sheka a shekarar 2018 daga APC.
Masu sharhi na ganin rikicin makiya da manoma na daga cikin abin da ya yi sanadin faduwarsa zabe.
Tun shekarar 2007 yake a matsayin Sanata.
Godswill Akpabio
Akpabio shi ne tsohon gwaman jihar Akwa Ibom. Ya zama sanata a shekarar 2015 karkashin jam’iyyar PDP.
A shekarar da ta gabata ne ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa mai mulkin kasar ta APC.
Jam’iyyar adawa ce ke mulkin jihar tasa.
A lokacin yakin neman zabe ya yi wa shugaban kasar Buhari alkawarin kuri’u miliyan 10 amma sanatan ya kasa kare tasa kujerar balle ya cika alkawarin da ya yi wa Buhari.
Suleiman Hunkuyi
Hunkuyi shi ne Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa.
Ya dare mukamin nasa a karkashin jam’iyyar APC kafin ya sauya sheka zuwa PDP a 2018 saboda fadan da yake yi da gwaman jiharsa, Nasiru Elrufa’i.
Abdu Kwari na APC ya kada shi da sama da kuriu 200,000.
Binta Garba Masi
Binta Masi ita kadai ce Sanata mace daga arewacin Najeriya a halin yanzu.
Ta zama sanata a shekarar 2015 karkashin jam’iyyar APC a mazabar Adamawa ta Arewa.
Ta rasa kujerarta inda dan takarar jam’iyyar PDP ya kada ita a zaben 23 ga watan Fabrairu da kimanin kuri’a 100.
Sanatocin Bauchi
Wasu fitattun sanatoci biyu daga jihar Bauchi Isa Hamma Misau na Bauchi Ta Tsakiya da da Nazif Gamawa na Bauchi ta Arewa na daga cikin wadanda Allah bai yi dawowarsu majalisar dattijan ba.
Sun hau kujerunsu a 2015 karkashin jam’iyyar APC, amma a shekarar 2018 suka yi sauyin sheka zuwa PDP tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.
Ba san ko yaya siyasar wadannan matasan sanatocin za ta kasance a gaba ba.

Abiola Ajimobi
Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya fadi zaben dan takarar Sanata a mazabar Kudu maso Yammacin jihar.
Mista Ajimobi, wanda shi ne gwamna mai ci na jam’iyar APC a jiharsa ya samu kuri’a 92,218.
Wanda ya lashe zaben shi ne Ademola Balogun na PDP da kuri’a 105,716.
Gwamna Ajimobi shi ne surukin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda dansa Idris Ajimobi ya auri Fatima Ganduje.
Ibrahim Hassan Dankwambo
Tsohon babban Akawun Tarayyar Najeriya wanda ya zama gwamnan jihar Gombe a shekarar 2011.
Duk da guguwar sak ta APC, Dankwambo ya yi nasarar rike kujerarsa a 2015.
Ya nemi kujerar Sanatan Gombe a 2019 ta Arewa amma bai yi nasara ba.
Sa’idu Alkali na APC ne ya kayar da shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More