Zaben 2019: Obasanjo na goyon bayan Atiku

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayana cewar wa tsohon mataimakin  shugaban kasa  kuman dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar  zaiyi aiki fiye da shugaba Buhari.

Obasanjo yace Atiku yana da kwarewa akan kasuwanci da nagartar da zai  yi mulki kuma ya samar wa  da matasa aiki yi a kasar ta Najeriya, idan yasumu nasarar lashe zaben 2019 mai  gabatowa.

Tsohon shugaban kasa yafadi hakane a yau Alhamis 11 ga watan Oktoba a saman karshe na benen gida sa cikin dakin karatusa a Abeokuta, Jahar Osun, anan ya bayana cewar ya yafe laifukan tsohon mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2003.

Obasanjo ya  kara  da cewar Atiku ya roke ya yafe masa, ya fadi haka ne a lokacin da fito da ganawa su ta sirra dasu ka  gudanar tare da Atiku, shugaban  jam’iyyar PDP Uche Secondus,malamin addinin kirista Bishop David Oyedepo,malamin addinin musulinci  Sheik Abubakar Gumil, tsohon gwamnan Jahar Osun Otunba Gbenga Daniel, , tsohon gwamnan  Jahar Cross Rivers Liyel Imoke tare da Sanata  Ben Murray Bruce  da kuma jagororin Afenifere da dai sauransu.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.