Zaben 2019:Yadda kotun koli ta kori daukaka karar Atiku

 

Kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar, a zaben da ya gabata na faburairu 2019, su ka yi.

Daukaka karar mai lamba SC/738/2019 an yi ta ne a bisa kalubalantar hukuncin da a ka yi a kotun sauraron kararrakin zabe, inda a ka yi hukunci da cewa, Atiku da PDP ba su da amsa a kan karar da su ka shigar a ranar 14 ga watan Mayu 2019 wacce jam’iyyar ta APC ta shigar, wanda ta neman a kori bukatar da Atiku da PDP su ka shigar ta kalubalantar nasarar da Shugaba Buhari ya samu a zaben shugaban kasa nay a gabata.

Cikin hukuncn da kotun kolin ta zartar na ranar Talata 20 ga watan Agusta 2019 kotun mai alkalai biyar, karkashin mai Shari’a Datijo Mohammed, ta yi watsi ne da daukaka karar gaba dayan ta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More