Zaben 2023: Oshiomhole da El’rufa’i a hotunan takarar shugaban kasa ya abun yake ne ?

A wani mataki mai daukan hankali, hotunan yakin neman zabe na takarar shugabancin kasar Najeriya dauke da hoton shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomole da kuma  gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai sun bayyana.

Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa fastocin sun fara yawo a yanzu haka a jahar Legas, inda tace ta yi ido hudu da ire iren hotunan nan a unguwar Surulere ta jahar Legas, da kuma yankin dake kusa da dandalin wasa na jahar Legas.

Hotunan takarar shugaban kasa na El-Rufai da Oshiomole sun bayyana Source: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a cikin wannan hoto dai an buga hoton shugaban APC, kuma tsohon gwamnan jahar Edo wato Adams Aliyu Oshiomole da sunan dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, yayin da hoton Malam Nasiru El-Rufai yake dauke da sunan dan takarar mataimakin shugaban kasar ta Najeriya.

Haka zalika wannan fasta yana dauke da wasu halaye guda 8 wadanda mabuga hotunan suka ce sune suka sanya mutanen biyu suka fi cancanta su tsaya takarar shugaban kasa da mataimaki a zaben 2023 domin gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daga cikin wadannan halaye da mabuga fastocin suka buga akwai:

– Mutane biyu da suke da halin biyayya

– Mutane biyu da suke da mutunci

– Mutane biyu masu son zaman lafiya

– Mutane biyu da suka amince da Dimukradiyya

– Mutane biyu da suke da gaskiya da rikon amana

– Mutane biyu da suka yarda da sauya fasalin Najeriya

– Mutane biyu da basu yarda da siyasar ubangida ba

– Mutane biyu da suka yarda da hadin kan Najeriya

Daga karshe an rubuta sunan wata kungiya mai suna ‘Miyatti Allah Cattle Breeders Association’ a matsayin wadanda suka buga wadannan fastoci.

Dama dai masana siyasar Najeriya na hasashen gwamnan jahar Kaduna zai iya fitowa takarar shugaban kasa, amma bai taba tabbatar da hakan a fili ba, kuma ko a yanzu bai ce komai game da wannan hoto ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More