Zaben Edo: Buhari ya taya Obaseki murna

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Gwamna Godwin Obaseki murnar nasarar da ya samu a zaben ranar Asabar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar a Jihar Edo.

Shugaba Buhari, yayin yaba wa tsarin zaben wanda ya kai ga nasarar Obaseki, ya bukaci Gwamnan da ya dawo ya nuna alheri da tawali’u.

Buhari ya ce “sadaukar da kaina ga zabuka cikin gaskiya da aminci, domin idan ba a gudanar da zabe na gaskiya da adalci ba, tushe na ikonmu na siyasa da dabi’a zai yi rauni,” in ji Buhari.

“Na yi ta bayar da goyon baya ga ganin an gudanar da zabe cikin gaskiya a kasar saboda shi ne tubalin tsarin dimokiradiyya na gaskiya.

“Dimokradiyya ba za tai tasiri ba idan kuri’un mutane ba’a kidaya su ba ko kuma idan aka yi amfani da hanyar zamba cikin aminci.”

Wannan sanarwa ce da babban hadiminsa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Lahadi, Shugaba Buhari ya kuma yaba wa mutanen jihar Edo, jam’iyyun, ‘yan takarar da kuma hukumomin tsaro kan yadda suka gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More