Zaben Kogi: APC na kulla makircin dage zabe – PDP

Kungiyar yakin neman zabe ta jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa akwai makirci da ake kullawa domin dage zaben mai gabatowa na  gwamnan jahar Kogi, wanda za’a  gudanar ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba 2019.

PDP ta zargi jam’iyyar APC da gwamnatin jahar Kogi da shirya makarkashiyar.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da mataimakin daraktan labarai na jam’iyyar  PDP Austin Okhai, ya aikewa yan jarida a ranar Laraba 12 ga watan Nuwamba, inda yake bayyana cewa APC da gwamnatin da Yahaya Bello ke jagoranta suna nan suna kamun kafa gabannin zaben, domin kuwa APC sai dai ta zo na uku a zaben da za’a gudanar a cewar sa.

Inda daga karshe Kungiyar kamfen din ta roki hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, kada ta yarda da duk wani yunkuri da zai saba abunda mutanen jahar ke tsammani.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More